News
Wani Matashi Ɗan Najeriya Ya Kashe Mahaifinsa, Ya Raunata ’Yan Uwansa Mata Biyu A Amurka
Wani matashi ɗan asalin Najeriya, Chukwuebuka Eweni, mai shekaru 27, ya shiga hannun jami’an tsaro a birnin New Orleans na ƙasar Amurka, bisa zargin kashe mahaifinsa tare da jikkata ’yan uwansa mata biyu a gidansu da ke unguwar Pebble.
Rahotanni sun bayyana cewa mahaifin matashin malami ne a fannin kimiyyar kwamfuta a Jami’ar Southern ta New Orleans.
Yerima Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Kwanaki Bayan Cacar Baka Da Wike
Iyayen matashin sun bayyana lamarin a matsayin abin girgiza, inda suka ce duk da cewa Chukwuebuka na fama da rashin lafiyar kwakwalwa, ba a taɓa samun sa da wani irin mummunan abu ba a baya.
AMINIYA ta tattaro cewa ɗaya daga cikin ’yan matan da suka jikkata an sallame ta daga asibiti, yayin da ɗayar ke kwance tana samun kulawar gaggawa.
Rundunar ’yan sandan New Orleans ta tabbatar da kama Chukwuebuka, inda ta ce ana duba lafiyarsa tare da ci gaba da gudanar da bincike kan al’amarin.
Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 9:59 na daren ranar 11 ga Nuwamba, 2025, bayan samun kiran gaggawa daga mazauna yankin. Jami’an da suka isa wurin sun tarar da mahaifin matashin ya mutu, yayin da sauran biyun suka samu raunuka masu tsanani.
A yanzu haka ana tuhumar Chukwuebuka da kashe mahaifinsa da kuma ƙoƙarin kashe ’yan uwansa mata guda biyu.
Ofishin Coroner na Orleans Parish ya ce zai fitar da cikakken sakamakon binciken gawar bayan kammala nazari.
