News
Kano: Gwamnati ta fara aikin sanya fitilun Kan Hanya A Dangoro
Gwamnatin Kano ta fara aikin saka fitilun kan tituna a yankin Dangoro da ke ƙaramar hukumar Kumbotso, matakin da mazauna yankin ke cewa ya kawo sabuwar rayuwa da ƙarin tsaro a wurin.
Mazauna Dangoro sun ce tsawon lokaci suna neman daukin gwamnati domin inganta tsaro da walwalar al’umma, musamman a daren da yankin kan kasance cikin duhu. Sun ce fara wannan aiki ya nuna gwamnatin Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf ta saurari kukansu.
Shugabar Tanzania Ta Bai Wa Sirikinta Da ’Yarta Muƙamin Minista
Wasu daga cikin jagororin al’umma sun ce yankin da a da ake tsoron fita da dare, yanzu ya koma kamar wuni saboda hasken da ake samu daga fitilun da aka kafa.
Shugaban kungiyar cigaban matasan yankin, Alhaji Muhammad Bashir Muktar na Dangoro Youth Development and Community Employment Association, ya ce aikin ya faranta wa al’umma rai matuƙa.
“Muna godiya ga Gwamnan Kano da Kwamishinan Ayyuka, Engr. Marwan, bisa cika alkawarin da suka yi. Yanzu yankin ya fara haske ta ko’ina kamar yadda muka dade muna fata,” in ji shi.
Haka zalika, wani jigo a yankin, Alhaji Umar Na Baruma, ya yaba da aikin fitilun da kuma ginin makarantar sakandare mai suna Engr. Abba Kabir Yusuf Government Girls Senior Secondary School, yana mai cewa aikin ya kawo canji mai ma’ana.
A gefe guda kuwa, al’ummar Dangoro sun sake rokon gwamnati da ta kammala aikin hanyar Dr. Danyaro Ali Muhammad Yakasai, wacce ke ratsa cikin garin, domin saukaka zirga-zirgar dalibai da mazauna yankin.
