News
Jami’an ’Yan Sanda Sun Cafke Tiktoka Da Ta Ƙirƙiri Labarin Sace Ta
Rundunar ’yan sandan jihar Edo ta kama wata mai amfani da TikTok, Osarobo Omoyemen — wadda aka fi sani da Madam Oil Rice — kan zargin ƙirƙirar labarin bogi cewa an sace ta domin ta jawo hankalin masu kallo a shafinta.
Omoyemen, mai shekaru 24, ta wallafa bidiyo da ya bazu sosai tana cewa wasu ’yan bindiga sun sace ta a kan titin Upper Sakponba da ke Benin City, sannan daga baya ’yan sanda suka ceto ta, suka tsare ta a ofishin Akpata Police Station, tare da tilasta ta biyan ₦10,000 kafin a sake ta.
ACF, Bashir Dalhatu and the Burden of Northern Unity, By Adnan Mukhtar
Sai dai rundunar ’yan sandan jihar ta ce wannan dukan labari ƙage ne tun daga tushe.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Moses Yamu, ya bayyana cewa sun fara bincike bayan bidiyon ya fara yawo a dandalin sada zumunta, kuma sakamakon ya tabbatar da cewa Omoyemen ta ƙirƙiro dukkan zancen ne domin jan hankalin jama’a.
A cewarsa: “Mun tabbatar da cewa duk bayanan ƙarya ne. An kama wadda ake zargi, kuma an gurfanar da ita a kotu ranar 20 ga Nuwamba, 2025. Haka kuma ana ci gaba da neman waɗanda suka taimaka mata wajen wannan yaudara.”
