Connect with us

News

Jami’an ’Yan Sanda Sun Cafke Tiktoka Da Ta Ƙirƙiri Labarin Sace Ta

Published

on

‎Rundunar ’yan sandan jihar Edo ta kama wata mai amfani da TikTok, Osarobo Omoyemen — wadda aka fi sani da Madam Oil Rice — kan zargin ƙirƙirar labarin bogi cewa an sace ta domin ta jawo hankalin masu kallo a shafinta.

‎Omoyemen, mai shekaru 24, ta wallafa bidiyo da ya bazu sosai tana cewa wasu ’yan bindiga sun sace ta a kan titin Upper Sakponba da ke Benin City, sannan daga baya ’yan sanda suka ceto ta, suka tsare ta a ofishin Akpata Police Station, tare da tilasta ta biyan ₦10,000 kafin a sake ta.

Advertisement

ACF, Bashir Dalhatu and the Burden of Northern Unity, By Adnan Mukhtar

‎Sai dai rundunar ’yan sandan jihar ta ce wannan dukan labari ƙage ne tun daga tushe.

Advertisement

‎Mai magana da yawun rundunar, CSP Moses Yamu, ya bayyana cewa sun fara bincike bayan bidiyon ya fara yawo a dandalin sada zumunta, kuma sakamakon ya tabbatar da cewa Omoyemen ta ƙirƙiro dukkan zancen ne domin jan hankalin jama’a.

Advertisement

‎A cewarsa: “Mun tabbatar da cewa duk bayanan ƙarya ne. An kama wadda ake zargi, kuma an gurfanar da ita a kotu ranar 20 ga Nuwamba, 2025. Haka kuma ana ci gaba da neman waɗanda suka taimaka mata wajen wannan yaudara.”

Advertisement

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending