News
Gwamnatin Birtaniya Ta Yi Watsi Da Bukatar Dawo Da Ekweremadu Nijeriya Domin Ya Kammala Zaman Gidan Yari
Gwamnatin Birtaniya (UK) ta yi watsi da bukatar gwamnatin tarayya na dawo da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu Nijeriya domin ya kammala tsawon shekarun da aka yanke masa na zaman gidan yari.
A halin yanzu, Ekweremadu yana zaman gidan yari a Birtaniya saboda hada baki wajen cire kodar wani matashi.
One Kano Agenda Ta Jinjinawa Gwamna Abba Kan Kasafin Kudin 2026 Na Naira Tiriyan 1 Da Biliyan 368
An yanke masa hukunci a watan Maris na 2023, inda aka yanke masa hukuncin shekaru tara da watanni takwas.
A farkon watan Nuwamba, Shugaba Bola Tinubu ya aika da wata babbar tawaga zuwa Landan don tattauna shari’ar Ekweremadu da kuma yiwuwar ya ci gaba da zaman gidan yarinsa a Nijeriya.
Tawagar ta kunshi Yusuf Tuggar, ministan harkokin waje, da Lateef Fagbemi, babban lauyan tarayya (AGF) kuma ministan shari’a.
Duk da haka, jaridar UK Guardian, wacce ta ambato wani jami’in ma’aikatar shari’a (MoJ), ta ruwaito cewa, an yi watsi da bukatar gwamnatin Nijeriya.
-
Opinion6 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion6 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
