Connect with us

News

‎One Kano Agenda Ta Jinjinawa Gwamna Abba Kan Kasafin Kudin 2026 Na Naira Tiriyan 1 Da Biliyan 368

Published

on

IMG 20251124 WA0281

Kungiyar One Kano Agenda ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa gabatar da kasafin kudin jihar na shekarar 2026 mai darajar Naira tiriliyan 1.368, wanda ta ce ya nuna tsari, jajircewa da himmar farfaɗo da tattalin arzikin Kano.

Amb. Abbas Yakasai ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Cibiyar ’Yan Jarida ta Jihar Kano (NUJ Press Centre) a ranar yau.

Advertisement

Shugaba Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Ɗaukar Ƴansanda 30,000

‎A cewar kungiyar, kasafin kudin ya nuna sahihin tsari domin an ware kashi 68% na kudaden zuwa aikin raya kasa, abin da ta ce ya wuce duk wani kaso da aka taba warewa a tarihin jihar.

‎Ga wasu daga cikin muhimman sassan da aka fi bai wa fifiko sune Ilimi – N405.3bn, Ayyukan more rayuwa – N346.2bn, Lafiya – N212.2bn

Advertisement

Kungiyar ta ce wadannan kudade za su taimaka wajen gina makarantu, inganta asibitoci, sabunta hanyoyi, da karfafa samar da ruwa a yankunan jihar.

‎One Kano Agenda ta kuma yaba wa gwamnan kan matsayinsa na tabbatar da cewa Kano ba mafaka ba ce ga masu aikata ta’addanci. Ta ce karin hadin kai tsakanin gwamnati, jami’an tsaro da kungiyoyin sa-kai ya taimaka wajen dakile matsalolin tsaro a birnin.

Advertisement

‎One Kano Agenda ta bukaci al’umma, musamman matasa da kungiyoyin farar hula, da su rika bibiyar yadda ake aiwatar da kasafin kudin domin tabbatar da cikakken amfani da kudaden ga jama’a.

‎Kungiyar ta roki Majalisar Dokokin Kano da ta yi nazari cikin hanzari kan kudirin kasafin kudin domin tabbatar da wucewarsa cikin lokaci, don a fara aiwatar da manyan ayyuka tun farkon shekarar 2026.

Advertisement

‎A cewar kungiyar, kasafin kudin 2026 nasara ce ta dukkan al’ummar Kano, musamman dalibai, manoma, mata, matasa, ‘yan kasuwa da ma’aikata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending