Kotu ta bayar da belin Beatrice Ekweremadu, matar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya Ike Ekweremadu a shari’ar da ake yi musu a birnin London
Ana yi wa Mista Ekweremadu, dan majalisar dattawan Najeriya da ka wakiltar Enugu ta yamma, tare da matarsa shari’a ne bisa zargin cire sassan jikin dan Adam a wata kotu da ke Burtaniya.
Jaridar the Cable, a Najeriya ta ruwaito cewa kotun ta bayar da belin Beatrice Ekweremadu ne bayan da ta bayyana a gaban kotun da ke birnin London.
Guguwa ta kashe mutum ɗaya da lalata gidaje 70 a Kano
To sai dai kotun ta hana belin mijin nata Mista Ekweremadu.
Ike Ekweremadu, mai shekara 60, da matarsa Beatrice Nwanneka Ekweremadu, mai shekara 55, sun gurfana a gaban kotun Majistiret ta yankin Uxbridge a Yammacin London.
