Connect with us

News

KAROTA ta cafke wasu matasa da makamai da kayan-maye a kano

Published

on

KAROTA

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

Advertisement

 

Hukumar KAROTA ta kama wasu bata garin matasa da makamai da kuma kayan shaye-shaye a shatale-talen gadar Dangi da ke birnin Kano.

Advertisement

 

Mai Magana da yawun hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Naisa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Talata .

Advertisement

An bayar da belin matar Ekweremadu

Nabilusi Abubakar, ya kuma ce guda cikin wadanda hukumar ta kama mai suna Mas’ud Ya’u Yusuf, ya shaidawa hukumar KAROTA cewa an kama su da su ne da kayan shaye-shaye da makamai.

Advertisement

 

Jami’an sintiri na hukumar ta KAROTA ne suka sami nasarar cafke matasan da daddare a karkashin shatale-talen Dangi, inda mutanen da aka kama suka bayyana akalla sun kai kwanaki hudu da shigowa garin Kano.

Advertisement

 

Sai dai binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa matasan sun shigo jihar Kano ne daga jihohin Katsina da Zamfara.

Advertisement

 

Tuni dai KAROTA ta bayyana bayan kammala binke ta mika mtasan hannun jami’an Yan sanda na ‘Yar Akwa domin faɗaɗa bincike tare da daukar mataki na gaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending