News
Gwamnatin Kano Ta Bukaci Jami’an Tsaro Su Kama Ganduje
Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci hukumomin tsaro su kama tsohon gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bisa kalaman da ya yi da ake ganin na iya kawo rikici a jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana haka yayin jawabi ga manema labarai kan sakamakon zaman majalisar zartarwa ta jihar.
Datti Baba-Ahmed Ya Ce Ayyana Dokar Ta-Ɓaci Kan Tsaro Da Shugaba Tinubu Ya Yi “Bai Da Amfani”
Kwamishinan ya ce, cikin kasa da awanni 48 bayan Ganduje ya bayyana niyyarsa ta kafa wata kungiyar sintiri, ‘yan bindiga sun kutsa cikin wani kauye a Kano inda suka yi garkuwa da mutane da dama.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta yaba da kokarin da Shugaba Bola Ahmad Tinubu ke yi na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, amma ta jaddada cewa duk wani furuci da ka iya tada tarzoma ba za a yi watsi da shi ba.
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News14 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
