Connect with us

News

Ibrahim Little Zai Garzaya Kotu Kan Yunkurin Ganduje Na Kafa Hisba Mai Zaman Kanta A Kano

Published

on

IMG 20251126 WA0003
Tsohon ɗan takarar gwamnan Kano, Ibrahim Ali Amin Little

Tsohon ɗan takarar gwamnan Kano, Ibrahim Ali Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke yi ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamna, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, na kafa wata Hisbah mai zaman kanta a jihar.

Little ya ce wannan yunƙuri barazana ne ga zaman lafiyar jihar, tare da iya haifar da rikice-rikice da rashin daidaito a tsarin tsaron al’umma.

Mataimakin Gwamnan Bayelsa Ya Rasu Sa’o’i Bayan Ya Yanki Jiki Ya Faɗi A Ofishinsa

Ya bayyana cewa ya umarci lauyoyinsa su aika wa masu wannan yunƙurin takardar gargadi, ya na shawartar su da su janye wannan tafiya nan take.

A cewarsa, idan suka ƙi bin umarnin, zai garzaya kotu domin dakatar da duk wani yunƙuri da zai iya haifar da rikici ko tarnaƙi ga tsarin doka a jihar

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending