News
An Samu Nasarar Ceto Dukiyoyin Da Darajarsu Ta Kai Naira Biliyan 1 Sakamakon Tashin Gobara A Kaduna
Hukumar Kashe Gobara da Tsaro ta Jama’a ta Jihar Kaduna ta ce an samu aukuwar gobara 50 tare da ceto dukiyoyi da darajarsu ya kai Naira biliyan 1.1 tsakanin Satumba da Nuwambar 2025.
Paul Aboi, Daraktan hukumar, ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Juma’a a Kaduna, inda ya ce gobarar ta faru a sassa daban-daban na yankunan Kaduna, Zaria da Kafanchan.
Kotu Ta Aike Da Tsohon Ministan Kwadago Chris Ngige Gidan Yari
Aboi ya ce an samu aukuwar gobara 50 cikin wadannan watanni uku, wanda ya haifar da mutuwar mutane biyu, raunin mutane 19, da kuma aikin ceto guda bakwai.
Ya kara da cewa an ceto dukiyoyi da kimarsu ya kai N1.1 biliyan, yayin da asarar da aka yi ya kai N2.7 biliyan, sakamakon gobara da suka faru a wuraren da ke cike da jama’a, unguwannin zama da wuraren kasuwanci.
A cewarsa, mafi yawan gobarar sun samo asali ne daga matsalolin wutar lantarki, sakaci wajen kula da wuta, da kuma adana kayan da suke iya kamawa da wuta ba tare da kiyaye wa ba, yana mai jaddada cewa hukumar ta rika gaggauta daukar mataki domin rage hasara da kare rayuka.
Aboi ya ce hukumar ta kara kaimi wajen wayar da kan jama’a, ta hanyar karfafa rundunonin gaggawa, tare da fadada fadakarwar al’umma domin rage aukuwar gobara, musamman a lokacin hunturu, wato (harmattan).
PREMIUM TIMES
-
News6 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News5 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News4 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
