Connect with us

News

Gwamnatin Kano ta Haramta Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Jihar

Published

on

Mun daina rusau sai dai mu kai mutum kurkurku kai tsaye Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da wata doka ta musamman da ta haramta kafa da gudanar da kowace kungiya mai kama da Hisbah da ba ta da izini, musamman wata kungiya da ta kira kanta da suna “Independent Hisbah Fisabilillahi.

Wannan doka mai taken “Dokar Gwamnatin Jihar Kano (Haramta Independent Hisbah Fisabilillahi) ta 2025,” Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya sanya wa hannu, kuma Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya karanta ta a taron manema labarai da ya kira a ofishinsa

Kotu Ta Aike Da Tsohon Ministan Kwadago Chris Ngige Gidan Yari

Ya ce Dokar ta samo asali ne daga Sashe na 5(2) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa gyara), wanda ke bai wa gwamnan jiha ikon gudanar da mulki da ya tabbatar da doka da oda a cikin jihar.

Ya kara da cewar Gwamnatin ta nuna damuwa matuka kan yadda wasu mutane da kungiyoyi ke gudanar da daukar ma’aikata, shirya taruka da kafa wata kungiya da suka kira “Independent Hisbah Fisabilillahi” ba tare da izini ba, kuma hakan ya saba wa dokokin Jihar Kano.

A cewar dokar, irin wadannan ayyuka na nufin kafa wata sabuwar hukuma ta tilasta bin doka ba bisa ka’ida ba a cikin jihar, wanda gwamnati ta bayyana a matsayin “aiki na haramtacciyar hanya da ke iya haddasa rikici” da kuma kawo cikas ga ayyukan hukumar Hisbah ta jihar.

Dokar ta bayyana a fili cewa “kafa Independent Hisbah Fisabilillahi ba bisa doka ba ne, kuma an haramta mata gudanar da kowanne irin aiki a cikin jihar.”

Advertisement

Gwamnati ta jaddada cewa hukumar Hisbah ta Jihar Kano ce kadai hukuma da doka ta amince da ita wajen gudanar da ayyukan Hisbah a jihar. Duk wani yunkuri na kwaikwayon ikon hukumar, kayan sanye, alamu ko ayyukanta yanzu an haramta su.

Kwamishinan Yada Labaran ya kuma ce, Dokar ta kuma umurci dukkan hukumomin tsaro da suka hada da Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya, Hukumar Tsaro ta DSS, da kuma NSCDC da su binciki wadanda suka shirya ko dauki nauyin wannan kungiya da aka haramta, su dakatar da duk wani aiki da ya shafi kungiyar, tare da daukar matakan doka don hana tayar da hankali.

Kwamared Waiya ya ce gwamnati ta bayyana cewa “shiga ko goyon baya ko alaka da kungiyar Independent Hisbah Fisabilillahi laifi ne a ƙarƙashin dokokin Jihar Kano.” An bukaci duk wanda aka riga aka dauka ko aka tuntuba don daukar aiki da ya janye kansa nan da nan kuma ya kai rahoto ga ofishin tsaro mafi kusa, ofishin Hisbah ko hukumar karamar hukuma.

“Duk wanda ya karya wannan doka zai fuskanci gurfanarwa a gaban kotu bisa laifukan da suka hada da taron doka ba bisa ka’ida ba, kwaikwayon ikon hukuma, da kafa wata hukuma ta tilasta bin doka ba tare da izini ba. Kalmar “Independent Hisbah Fisabilillahi” ta hada da kowace kungiya, rukunin mutane, kwamiti, motsi ko wata kungiya da aka kafa domin gudanar da ayyukan Hisbah ba tare da amincewar hukumar Hisbah ta doka ba.”

“Wannan doka ta fara aiki nan take kuma za a wallafa ta a jaridar gwamnati ta Jihar Kano. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya wa dokar hannu a ranar 8 ga Disamba, 2025, a matsayin wani muhimmin mataki na daidaita harkokin Hisbah a ƙarƙashin doka da hana yaduwar kungiyoyin sa kai marasa izini.” In ji Kwamishinan Yada Labarai

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending