Politics
Kungiyar Matasan APC Ta Yi Kira Ga Kwankwaso Da Gwamna Abba Su Dawo Jam’iyyar APC
Kungiyar Northern Youths APC New Era ta yi kira ga fitattun jagororin siyasar Arewa, ciki har da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da su sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a Kano wanda Muhammad Rabiu Mustapha jagaranta, inda ta ce shigowar waɗannan shugabanni APC zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai da ci gaban ƙasa.
Kungiyar Matasan APC Ta Yi Kira Ga Kwankwaso Da Gwamna Abba Su Koma Jam’iyyar APC
A cewar matasan, APC jam’iyya ce da ta samo asali daga haɗewar wasu jam’iyyun siyasa daban-daban, kuma tun daga kafuwarta take aiki domin nasarar Najeriya.
Kungiyar ta ce gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ɗaukar matakai masu wahala amma masu muhimmanci, duk da ƙalubalen tattalin arzikin da ƙasar ke fuskanta.
Sun ce gwamnatin ta mai da hankali wajen gyaran tattalin arziki, inganta ababen more rayuwa da kuma samar da tallafi ga wasu sassan al’umma domin rage radadin rayuwa.
A yayin taron, kungiyar ta bayyana Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagororin Arewa da suka rike mukamai daban-daban a Najeriya, tare da bayar da gudunmawa a harkokin siyasa da mulki.
Haka kuma, ta ce Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na daga cikin shugabannin da ke da kwarewa a harkokin mulki, inda ta bayyana cewa shigarsa APC zai iya kawo sabbin sauye-sauye ga jihar Kano.
Kungiyar ta ce Najeriya ƙasa ce mai cike da kabilu da yankuna daban-daban, inda ta jaddada cewa haɗin kai tsakanin shugabanni daga sassa daban-daban na ƙasar ne zai tabbatar da cigaba mai ɗorewa.
A ƙarshe, kungiyar ta ce ta yi wannan kira ne bisa la’akari da makomar ƙasa da kuma bukatar haɗin kan ‘yan siyasa wajen tinkarar manyan ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta.
