Connect with us

News

Jami’an ‘Ƴansanda Sun Tabbatar Da Sace Mutane Sama Da 160 A Kaduna

Published

on

Rundunar ƴansandan Najeriya ta janye matsayarta ta farko na cewa babu sahihan bayanai kan rahotannin sace mutane a ƙauyen Kurmin Wali da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna, inda yanzu ta tabbatar da cewa an yi garkuwa da mutane masu yawa a yankin.

Rahotanni sun fara bayyana ne a ranar Litinin cewa wasu mahara sun kai farmaki ƙauyen tare da sace kimanin mutum 170.

Advertisement

Sojoji Sun Dakile Harin Kwanton Bauna A Zamfara, Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama, Sun Rasa Jami’ai Shida

A wancan lokaci, rundunar ƴansandan ta bayyana cewa ba ta da hujjojin da za su tabbatar da irin waɗannan rahotanni, tana mai kiran su a matsayin labaran ƙarya.

Advertisement

‎Sai dai a wata sanarwa da ta fitar cikin daren Talata, rundunar ta ce an yi kuskuren fahimtar sanarwar ta farko, inda ta bayyana cewa manufarta ita ce neman sahihan bayanai kan sunayen mutanen da aka sace da kuma inda aka ɗauke su.

‎Kakakin rundunar ƴansandan, Benjamin Hundeyin, ya ce binciken da sashen tattara bayanan sirri na rundunar ya gudanar ya tabbatar da cewa an yi garkuwa da mutanen.

Advertisement

‎“Bincikenmu ya tabbatar da cewa an sace mutane a yankin. Tuni muka tura jami’ai zuwa Kajuru da kewaye domin gano inda ake tsare da su da kuma tabbatar da ceto su,” in ji Hundeyin.

‎Tun da farko, sarkin Kurmin Wali, Ishaku Dan’azumi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce maharan sun kai harin ne a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 9 na safe, lokacin da jama’a ke tsaka da ibada.

Advertisement

‎“Sun shigo lokacin da muke coci, suka bazu a garin, suka kewaye mu. Waɗanda ke hannunsu yanzu su 166 ne,” in ji shi.

‎Shi ma shugaban ƙungiyar Kiristoci ta CAN a Arewacin Najeriya, Joseph Hayab, ya ce bayanan da ya samu daga yankin sun nuna cewa kusan mutum 172 aka sace, inda mutum tara suka tsere, yayin da ake ci gaba da neman wasu 163.

Advertisement

‎Wasu mazauna Kurmin Wali sun shaida wa manema labarai cewa an kai harin ne a coci-coci uku, ciki har da cocin Pentecostal Fellowship Assembly (PFA) guda biyu da kuma cocin Evangelical Church Winning All (ECWA).

‎A cewarsu, mutane 177 aka sace, amma 11 daga cikinsu sun samu tserewa, yayin da kimanin 160 ke hannun maharan.

Advertisement

‎Wani ganau ya ce: “An kai harin ne da misalin ƙarfe 10 na safiyar Lahadi. Wasu sun yi yunƙurin tserewa, amma sun kasa saboda yadda maharan suka kewaye ƙauyen da makamai.

‎Daga bisani sun tara mutane wuri guda sannan suka shige daji da su.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending