News
Jami’an Ƴan Sanda Sun Kama Masu Siyar Da Jarirai AEkiti
Rundunar ƴan sandan Jihar Ekiti ta ce ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da shiga harkar kebe mata domin haifar da jarirai da nufin sayar da su, tare da ceto ƙananan yara shida a Ikere-Ekiti.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Joseph Eribo, ya bayyana hakan a ranar Talata a Ado-Ekiti, inda ya ce samamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da rundunar ta samu.
Yan Najeriya Na Shan Fiye Da Lita Biliyan 2.5 Na Ruwan Leda A Duk Shekara — Gwamantin Tarraya
Eribo ya ce bincike ya nuna cewa wata mata mai suna Oluwadare Onyechi, ‘yar shekara 43, na tafiyar da wani gida da ke bayan otal ɗin Inisa a layin Ise-Ekiti, inda take killace mata domin su rika haifar da jarirai ana saida su.
Ya ce jami’an tsaro sun kama Onyechi tare da wasu mutane huɗu da suka haɗa da Onuoha Gloria (28), Ihegbogu Mercy (21), Emmanuel Esther (23), mai juna biyu, da Victoria Linus.
Ƴan sandan sun ceto ƙananan yara shida masu shekaru tsakanin 2 zuwa 9, tare da ƙwato wasu kwayoyin maganin dexamethasone da kuma kwalaben man Goya, waɗanda ake zargin ana amfani da su wajen aikata laifin.
Kwamishinan ya ce an fara zurfafa bincike kan lamarin, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.
An Kama Barayin Shanu 17, An Kwato Shanu 558
A wani ɓangare na samamen, rundunar ta kuma kama barayin shanu 17, tare da kwato shanu 558 da ake zargin an sace su a jihohi daban-daban.
Eribo ya ce a ranar 21 ga Janairu jami’an tsaro sun kama wani da ake zargi da kasancewa shahararren barawon shanu, Ibrahim Abubakar, wanda ya amsa cewa ya dade yana sace shanu a jihohin Ekiti, Kwara da Kogi.
Ƴan sandan sun kwato shanu 255 daga hannunsa, yayin da aka ƙwato shanu 303 daga hannun wasu mutum 16 da aka kama a wasu wurare daban-daban a jihar.
Ya ce waɗanda ake zargin sun kasa bayar da gamsasshen bayani kan yadda suka mallaki dabbobin, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.
Rundunar ƴan sandan ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai wajen daƙile laifuka a fadin jihar, tare da kira ga al’umma da su rika bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro.
