Connect with us

News

Jirgin Sojin Sama Ya Hallaka Manoma Biyu ‘Bisa Kuskure’ A Neja

Published

on

Wani Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Hallaka Mutane Da Dama A Sokoto 

Aƙalla manoma biyu sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama, ciki har da ƙananan yara, suka jikkata sakamakon wani hari ta sama da aka kai garin Kurgi, da ke ƙaramar hukumar Mariga a Jihar Neja.

Mazauna yankin sun shaida cewa wani jirgin sama mai aikin bincike, wanda ake zargin na rundunar sojin saman Najeriya ne, ya yi ta shawagi a sararin samaniya na tsawon wasu mintuna a ranar Lahadi, kafin daga bisani ya buɗe wuta kan mutanen da ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Advertisement

Jami’an Ƴan Sanda Sun Kama Masu Siyar Da Jarirai AEkiti

A cewar wani mazaunin yankin, harsasai sun afka har cikin gidajen jama’a, lamarin da ya haddasa jikkatar mutane da dama, ciki har da yara ƙanana.

Advertisement

Wani mazaunin yankin, Suleiman Sanusi, ya ce harin ya haifar da fargaba da firgici a tsakanin al’umma, inda da dama suka tsere zuwa garin Bangi da wasu yankuna da suka fi samun tsaro.

Ya bayyana lamarin a matsayin abin ba-zata, yana mai kira ga hukumomi da su gaggauta bincike, tare da samar da agajin lafiya ga wadanda suka jikkata.

Advertisement

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar sojin saman Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin.

 

Advertisement

DAILY TRUST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending