News
Buhari Ne Ya Sanya Abba Yusuf Ya Zama Gwamna A 2023 — Buba Galadima
Wani jigo a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Buba Galadima, ya ce marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf a zaɓen gwamnan Jihar Kano na shekarar 2023.
Galadima, wanda shi ne Sakataren Kwamitin Amintattu (BoT) na NNPP, ya bayyana cewa tsayuwar Buhari ta taimaka wajen hana maimaita abin da ya kira “kwace nasara” da ya faru a zaɓen 2019, inda jam’iyyar APC ta karɓi mulkin jihar.
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wani Matashi Kan Zargin Sa Da Daddatsa Mahaifinsa Da Adda
Da yake magana a wata hira da tashar Arise News, Galadima ya ce Buhari bai goyi bayan duk wani yunƙuri na hana NNPP cin moriyar nasarar da ta samu ba, musamman saboda rashin jituwar da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
A cewarsa, Ganduje ya taba cin mutuncin Buhari a fili, duk da rawar da tsohon shugaban ƙasar ya taka a siyasar Kano a baya, lamarin da ya sa Buhari ya ƙi mara wa duk wani shiri na sake kwace nasarar NNPP baya a 2023.
Galadima ya kuma yi ikirarin cewa a zaɓen 2019, an samu katsalandan daga wasu bangarori na hukumomin tsaro da na shari’a, amma wannan karon Buhari ya nace cewa dole a mutunta zaɓin jama’a domin kauce wa rikici da zubar da jini a Kano.
Ya ƙara da cewa hukuncin kotuna a matakai daban-daban ya tabbatar da nasarar Abba Yusuf, yana mai cewa wannan ya nuna cewa an yi ƙoƙarin barin sakamakon zaɓe ya tsaya, tare da bai wa adalci dama.
DAILY POST
