News
Gobara Ta Tashi A Gidan Mai A Kano
Wata gobara ta tashi a gidan Man Jamilu Inusa Petroleum da ke Unguwar Samegu, kusa da Sani Abacha Youth Centre a yankin Kazama na Jihar Kano, inda ta janyo asarar dukiya, sai dai ba a samu asarar rai ba.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta tashi ne a daren ranar Juma’a, yayin da ake kokarin sauke man fetur daga wata motar dakon mai, inda motar ta kama da wuta, lamarin da ya haddasa yaduwar gobarar zuwa wasu kadarori da ke kusa.
KPCF Ta Nesanta Kanta Daga Zargin Kalaman Batanci Da Wariya Da Aka Dangantawa Abdussalam Kani
Shaidun gani da ido sun ce gobarar ta haddasa ƙonewar mota guda ɗaya da wani ginin kasuwanci (plaza), lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici.
Wani mazaunin unguwar ya shaida wa wakilinmu cewa, “Lamarin ya faru ne ba zato ba tsammani. Jama’a sun rika fitar da mata da yara daga gidaje domin kare rayukansu kafin isowar jami’an kashe gobara.”
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
