News
KPCF Ta Nesanta Kanta Daga Zargin Kalaman Batanci Da Wariya Da Aka Dangantawa Abdussalam Kani
Ƙungiyar Kano Patriotic Coalition of Civil Society Organisations Forum (KPCF) ta bayyana cewa ba ta da alaƙa da kalaman nuna wariya da ake zargin Dr. Abdussalam Kani ya yi kan mambobin masu buƙata ta musamman (PWDs) a Jihar Kano.
A wata sanarwa da Hassan Ibrahim Gama, Mustapha Muhammed Chiroma da Peter Hassan Tijjani suka rattaba wa hannu, ƙungiyar—wadda ta haɗa sama da ƙungiyoyin farar hula 310—ta ce ta karɓi rahotannin da suka shafi lamarin ne cikin matuƙar damuwa.
KPCF ta jaddada cewa ba ta goyon baya, ba ta karewa, kuma ba ta lamuntar kowace irin nuna wariya, tsoratarwa ko cin mutunci ga kowane mutum ko rukuni, ba tare da la’akari da nakasa, asali, addini ko ra’ayi ba.
Ƙungiyar ta ce aikin kungiyoyin farar hula ya ta’allaka ne kan haƙuri, girmama bambancin al’umma da haɗin kai, tana mai cewa duk wani hali da ke tauye waɗannan ginshiƙai ya saɓa da ruhin dimokuraɗiyya da zaman tare.
Ta kuma nuna damuwa kan zargin da ke cewa an yi wa mambobin masu buƙata ta musamman barazana, cin zarafi da kalaman raini, tana mai jaddada cewa mutanen da ke da nakasa cikakkun ’yan ƙasa ne, kuma wajibi ne a mutunta haƙƙinsu na shiga muhawarar jama’a.
A cewar ƙungiyar, duk wani yunƙuri na tauye ko tozarta mutuncin masu nakasa ya saɓa da kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa kan kare haƙƙin ɗan Adam.
KPCF ta ce ta nesanta kanta gaba ɗaya daga duk wani kalami ko ɗabi’a na nuna wariya da ake dangantawa da Dr. Abdussalam Kani, tare da bayyana goyon bayanta ga Mista Michael Nworisa da sauran mutanen da abin ya shafa.
