Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Ƙwato Zunzurutun Kuɗi Naira Miliyan 37 Da Za A Kai Wa Ƴan Bindiga A Borno

Published

on

FB IMG 1771280843043

Dakarun rundunar haɗin gwiwar sojin Najeriya, Operation HADIN KAI, sun kwace kuɗi har naira miliyan 37 da ake zargin an shirya kai wa ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Dakarun Sojin sun kama kuɗin ne a wani shingen bincike da ke sansanin Forward Operating Base (FOB) Chabbal a jihar Borno, bayan sun tare wata mota mai ɗauke da mutane biyar — maza uku da mata biyu — da ake zargi da hannu a safarar kuɗaɗen.

Advertisement

Wasu Gungun Fusatattun Matasa Sun Kone Wanda Ake Zargi Da Satar Babur 

‎A cewar majiyoyin soji, an gano kuɗin da aka ɓoye a cikin jakunkuna, tare da wayoyin salula da dama da ake zargin suna da alaƙa da sadarwa da daidaita ayyukan ‘yan ta’adda.

Advertisement

‎Ana ci gaba da yi wa waɗanda aka kama tambayoyi, yayin da ake nazarin kayayyakin da aka ƙwato domin tattara bayanan sirri.

‎Jami’an soji sun bayyana cewa kwace kuɗin wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin lalata hanyoyin samun kuɗaɗen da ke tallafa wa ayyukan ta’addanci a yankin, ciki har da ƙungiyar ISWAP.

Advertisement

 

Advertisement

PRNIGERIA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending