Connect with us

News

Sabuwar Gobara Ta Tashi A Wata Kasuwa A Kano, Ta Ƙone Shaguna 50

Published

on

Wata gobara da ta tashi da asubahin ranar Juma’a ta ƙone aƙalla shaguna 50 a Kasuwar Fatima Simra Multi-Purpose da ke yankin Dakata a Jihar Kano.

Shugaban kwamitin kashe gobara na kasuwar, Dauda Haruna Chula, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 5:40 na safe, kuma har zuwa lokacin tana ci gaba da yaɗuwa.

Advertisement

Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A Watan Ramadan A Tarihin Musulunci

Ya bayyana cewa galibin shagunan da abin ya shafa ƙanana ne da ke harkar sarrafa mai da kuma sake sarrafa robobi da leda. A cewarsa, an sanar da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki, waɗanda suka tabbatar da samun bayanin faruwar gobarar.

Advertisement

Har yanzu ba a tantance girman asarar da aka yi ko yiwuwar asarar rayuka ba, yayin da ‘yan kasuwa ke nuna damuwa kan jinkirin kai ɗauki. Lamarin na zuwa ne mako guda bayan wata babbar gobara ta shafi ‘yan kasuwa sama da 1,000 a Kasuwar Singa a Kano.

 

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending