News
Ƙungiyar Kare Haƙƙin Dan Adam Ta Yi Allah-Wadai Da Zargin Cin Zarafin Ɗan Jarida A Kano
Ƙungiyar GLOBAL COMMUNITY FOR HUMAN RIGHTS NETWORK NIGERIA ta yi kakkausar suka kan zargin cin zarafin ɗan jarida Abdulbaki Ali Ahmed Sharifai, wanda ake cewa wani jami’in gwamnatin Jihar Kano, Auwal Sani Rogo (SSR), ya aikata a yayin wani taro da ya shafi gasar kamun kifi da aka gudanar a Argungu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta bayyana cewa lamarin ba wai cin mutuncin mutum ɗaya kaɗai ba ne, illa hari ne kai tsaye ga ’yancin aikin jarida da kuma ’yancin faɗin albarkacin baki — ginshiƙan dimokuraɗiyya.
Amurka Ta Buƙaci Najeriya Ta Katse Cinikin makamai da Rasha
Ƙungiyar ta ce abin takaici ne yadda al’amarin ya faru a gaban manyan jami’an gwamnati, amma har yanzu babu wata hukunci ko neman afuwa daga wanda ake zargi ko daga gwamnatin jihar, lamarin da ta ce na iya nuna rashin mutunta doka da kuma yunƙurin danne ’yan jarida.
Ƙungiyar ta bai wa gwamnatin Jihar Kano wa’adin sa’o’i 24 domin ladabtar da wanda ake zargi,bayar da hakuri a hukumance ga ɗan jaridar,da kuma tabbatar da kariya ga ’yan jarida a jihar.
Ta ce idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, za ta garzaya kotu domin neman cikakken haƙƙin wanda aka ce an ci zarafinsa.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci kwamishinan ’yan sandan jihar da ya gudanar da bincike tare da gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu. Ta ce tana da sahihan bayanai cewa an shigar da ƙorafi, amma wanda ake zargi bai amsa gayyatar da aka yi masa ba.
A cewar sanarwar, wannan ba shi ne karo na farko ba da ake zargin cin zarafin ɗan jarida a jihar. Ta ambaci wani lamari makamancin haka da ya shafi Aminu Halilu Tudunwada, tana mai cewa hakan na nuna yadda matsalar ke ƙara kamari.
Ƙungiyar ta yi kira ga ƙungiyoyin kare haƙƙin dan Adam, ƙungiyoyin ’yan jarida, lauyoyi da masu rajin dimokuraɗiyya, da kuma al’umma baki ɗaya da su tashi tsaye domin kare martabar aikin jarida.
“’Yancin jarida ba laifi ba ne — ginshiƙi ne na adalci da gaskiya. Duk wanda ya ci zarafin ɗan jarida, ya ci zarafin al’umma baki ɗaya.”
