Connect with us

News

Kotu Ta Yanke Wa Wani Matashi  Hukuncin Daurin Shekaru 20 A Gidan Yari A Kano  ‎

Published

on

Kano State High Court 768x372

Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai shekaru 25 hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari bayan samunsa da laifin kashe kawunsa sakamakon rikici kan gona.

‎Wanda aka yankewa hukuncin, Bara’u Sa’idu, mazaunin Jarimawa dake Ƙaramar Hukumar Bagwai a Kano, an gurfanar  dashi ne gaban kotu bisa zargin kisan kai, amma tun da farko ya musanta aikata laifin.

Advertisement

ƘARFIN HALI: Wani Mutum Ya Kira ’Yan Sandan Kano Don Sanin Ko Sunansa Na Cikin Jerin Dillalan Miyagun Ƙwayoyi

‎Masu gabatar da kara sun shaida wa kotu cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar 7 ga Agustan 2021, inda rikici ya barke tsakanin Sa’idu da kawunsa, Magaji Yusuf, mai shekaru 64, kan wata matsala da ta shafi gona.

Advertisement

‎A cewarsu, Sa’idu ya buge marigayin da sanda a kai, lamarin da ya jawo masa munanan raunuka, ciki har da rasa ido guda, wanda daga bisani ya yi sanadin mutuwarsa.

‎Da yake kare kansa, Sa’idu ya shaida wa kotu cewa bai yi niyyar kashe kawunsa ba, yana mai cewa ya bugi marigayin ne domin kare kansa yayin rikicin.

Advertisement

‎Sai dai a hukuncin da ta yanke, Mai shari’a Justice Maryam Sabo ta ce hujjojin da masu gabatar da kara suka gabatar sun tabbatar da laifin wanda ake kara ba tare da kokwanto ba.

‎Kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 bisa tanadin dokar Penal Code ta Jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending