Connect with us

News

Kotu Ta Yankewa Wasu Alƙalai Hukuncin Watanni 36 A Gidan Yari

Published

on

kotu

Kotu a Burkina Faso ta yankewa wasu manyan alƙalan kotun Majistare huɗu da jami’an hukumar fasa ƙwauri 3 hukuncin watanni 2 zuwa 36 a gidan yari sakamakon samunsu da cin hanci da rashawa.

Bayan gudanar da bincike na kwanaki da alƙali Jean Jacques Wend-Panga ya jagoranta, kotun ta samu alƙalan 4 da lafin karɓar cin hanci da rashawa tare da watsi da ƙarar da aka shigar kan jami’an na custom game da karɓar cin hanci, wannan yasa kotun yanke wa Alban Balanoe Some zaman gidan waƙafi na watanni 36 sai Mohamed Traore da Urbain Medah da Sandaogo Antoine Kabore da aka yankewa hukuncin zaman gidan yari na watanni biyu zuwa goma sha biyu tare da biyan tara tsakanin CFA miliyan biyu zuwa uku.

Gwamnatin Kano Ta Haramta Zuba Yashi Da Sauran Kayan Gini A Kan Titunan Jihar 

A ɓangaren jami’an fasa ƙwaurin da suka haɗa da Oumarou da Jonas Yameogo da Zindi Nikiema kotu ta yanke musu zaman gidan yari na tawon watanni goma sha biyar da ƙarin watanni biyu na karɓar cin hanci.

A yayin sauraron ƙarar, alƙalin kotun ya ƙi amince wa da tuhumar masu laifin na garkuwa da azabtar da su a lokacin da suke tsare ana bincike.

 

Advertisement

 

RFI

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending