Connect with us

Business

Matatar Dangote Ta Ƙara Farashin Man Fetur Zuwa N1,175, Karo Na Uku Cikin Mako Guda

Published

on

FB IMG 1773006543246

Matatar man fetur ta Dangote ta sake ƙara farashin fetur zuwa Naira 1,175 kan kowace lita, a wani sabon sauyi da ya zama karo na uku cikin mako guda

Sabon ƙarin farashin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar cewa farashin kayayyaki da ayyuka a faɗin Nijeriya zai ci gaba da ƙaruwa sakamakon tashin farashin man fetur, wanda ke da tasiri kai tsaye kan sufuri da harkokin kasuwanci.

Advertisement

Tirela Ta Murkushe Mutum 3 A Kano 

Rahotanni sun nuna cewa matatar ta sanar da ‘yan kasuwa sabon farashin ne a ranar Litinin, inda ta ɗaga farashin zuwa N1,175 kan kowace lita, daga N995 kan kowace lita da aka sanar a ranar Juma’a. Wannan na nufin an samu ƙarin Naira 180 cikin ‘yan kwanaki kaɗan.

Advertisement

Wannan mataki ya biyo bayan wani rahoto da jaridar THE PUNCH ta wallafa, inda ta yi hasashen cewa farashin fetur na iya sake tashi karo na uku cikin mako guda, musamman bayan dakatarwar wucin gadi da matatar Dangote ta yi kan sayar da fetur a ranar Lahadi.

Masana tattalin arziki sun yi gargadin cewa sabon ƙarin farashin na iya ƙara tsananta matsin rayuwa ga ‘yan Nijeriya, domin farashin sufuri, abinci da sauran kayayyaki na iya tashi.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending