Connect with us

News

Jami’ar BUK Ta Fara Binciken Ɗalibin Da Ake Zargi Da Amfani da Sunan Mata Wajen Damfarar Jama’a

Published

on

buk new 3

Jami’ar Bayero University Kano (BUK) ta sanar da fara bincike kan wani ɗalibi da ake zargi da amfani da sunan mace wajen damfarar mutane da sunan neman tallafin kuɗin makaranta.

Gwamnatin Kano za ta shirya bikin al’adu na Eid Fest tare da rabon na’urorin POS ga matasa

Advertisement

Rahotanni sun bayyana cewa ɗalibin na amfani da wasu sunayen mata a kafafen sada zumunta domin yaudaran jama’a, inda yake gabatar da kansa a matsayin ɗaliba mai fama da matsalar rashin kuɗin biyan kuɗin makaranta. Ta wannan hanya ne ake zargin yana roƙon mutane su tura masa kuɗi a matsayin taimako.

Majiyoyi sun ce bayan samun korafe-korafe daga wasu mutane da suka ce an damfare su, jami’ar ta ɗauki matakin fara bincike domin gano gaskiyar zargin da kuma daukar matakin da ya dace.

Advertisement

Wata majiya daga cikin jami’an jami’ar ta ce mahukunta ba za su lamunci duk wani abu da zai bata sunan jami’ar ba, tare da jaddada cewa za a hukunta duk wanda aka samu da laifi bisa ƙa’ida.

Jami’ar ta kuma yi kira ga ɗalibai da sauran jama’a da su rika yin taka-tsantsan da irin waɗannan sakonni na neman taimako a shafukan sada zumunta, musamman idan ba su da tabbacin sahihancin wanda ke neman tallafin.

Advertisement

Ana sa ran sakamakon binciken da jami’ar ke gudanarwa zai bayyana gaskiyar lamarin tare da fayyace matakin da za a ɗauka kan wanda ake zargi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending