News
Gwamnatin Kano za ta shirya bikin al’adu na Eid Fest tare da rabon na’urorin POS ga matasa
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da shirin gudanar da wani babban bikin nishadi da al’adu mai suna Eid Fest, wanda za a yi a ranar 28 zuwa 29 ga watan Maris na shekarar 2026 a filin wasa na Sabon gari dake jihar.
Sanarwar ta fito ne daga ofishin mai bai wa gwamnan jihar kano shawara kan harkokin matasa da wasanni Hon. Sani Musa Danja.
Miliyoyin Yara Fama Da Yunwa Sakamakon Tashe Tashen Hankula A Najeriya
Bikin zai kunshi abubuwa da dama da suka hada da hawa doki, kasuwar abinci, kide-kide, wasanni, zanen lalle da sauran nishadi domin hada kan matasa da iyalai a lokacin bukukuwan Sallah.
Hakazalika, shirin zai kasance wata dama ta bunkasa tattalin arziki ga matasa da kananan ‘yan kasuwa a fadin jihar.
A karkashin shirin, za a kaddamar da wani tsari na tallafa wa matasa da kananan ‘yan kasuwa da na’urorin POS kyauta, domin taimaka musu shiga harkokin hada-hadar kudade ta zamani da kuma fadada sana’o’insu.
Ana aiwatar da wannan shiri ne tare da hadin gwiwar bankin Alternative, domin karfafa shigar jama’a cikin tsarin hada-hadar kudade da kuma bunkasa sana’o’in matasa.
Mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin matasa da wasanni, Sani Musa Danja, ya ce shirin ya yi daidai da manufofin gwamnatin jihar na tallafa wa matasa da kananan ‘yan kasuwa domin bunkasa tattalin arzikin jihar.
Ya kara da cewa wannan mataki na daga cikin kudirin gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, na inganta rayuwar matasa da tabbatar da shugabanci mai hada kan jama’a.
An kuma bukaci matasa da kananan ‘yan kasuwa da su halarci bikin domin cin gajiyar damar tallafin da aka tanada.
Sanarwar ta ce shiga bikin Eid Fest kyauta ne ga masu asusun banki na Alternative Bank.

