Connect with us

News

Miliyoyin Yara Fama Da Yunwa Sakamakon Tashe Tashen Hankula A Najeriya 

Published

on

Yaran da ke fama da yunwa da UNICEF ke kula da su a Sabuwar Marte a Jihar Borno
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Ƙungiyar agaji ta ICRC ta ce kusan yara miliyan 6,400,000 ke fama da tamowa ko rashin abinci mai gina jiki sakamakon tashe tashen hankulan da aka kwashe shekaru ana tafkawa.

Sanarwar da ƙungiyar ta fitar yau ta ce waɗannan rikice rikice sun haɗa da waɗanda ake yi na boko haram a arewa maso gabas, da na ƴan bindiga a arewa maso yamma, da kuma rikicin manoma da makiyaya a arewa ta tsakiya.

Gwamnan Kano ya sauke shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Abdullahi Musa daga mukaminsa

Ƙungiyar ta sanar da cewar ƴara ƙanana da mata su suka fi fuskantar wannan matsalar ta Yunwa, yayin da kai wa gare su a yankunan da suke ke da matukar wahala musamman a jihohin Borno da Yobe.

Tashe tashen hankulan da suka hana mutane zuwa gonakin su sun taimaka wajen haifar da ƙarancin abinci, a dai dai lokacin da ƙungiyoyin agaji ke fuskantar ƙarancin kuɗaɗen aiki, yayin da matsalolin jinkai kuma ke ƙaruwa.

Ƙungiyar ta ce ƙaruwar matsalar tamowa na matuƙar buƙatar ɗaukin gaggawa, abinda ya sa ICRC ta rungumi shirin kula da lafiyar masu fama da cutar da kuma samar da tsabtacacen ruwan sha da tallafin kayan abinci mai gina jiki ga waɗanda ke fama da matsalar.

Advertisement

Ƙungiyar ICRC ta ce akalla mutane 348,000 cikin su harda yara 16,000 da mata 19,000 suka samu kulawa a cibiyoyin kula da lafiyar ICRC dake jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe, baya ga al’ummomi 125 da suka samu tallafin abinci yara mai gina jiki.

ICRC ta ce a bara, mutane sama da 17,000 suka samu tallafin kuɗaɗe daga ƙungiyar har sau uku domin sayen abinda za su ci.

Ƙungiyar ta kuma bayyana taimakawa mutane sama da 168,000 da kayan noma da suka haɗa da iri da injin din ban ruwa da wasu kayan aiki domin samarwa kan su abinci.

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending