News
Zamfara: Jami’an Tsaro Sun Kama Matashi Da Harsashi 800 Da Ya Ɓoye A Tankin Babur
Jami’an tsaro a jihar Zamfara sun kama wani matashi mai shekaru 25 da ake zargi da safarar harsasai 800 na bindigar AK-47, bayan ya ɓoye su a cikin tankin man babur.
Rahotanni sun nuna cewa an kama matashin, Mannir Adam, da misalin ƙarfe 7:50 na yammacin ranar Talata a kan hanyar Gusau zuwa Funtua, yayin da jami’an tsaro ke gudanar da binciken ababen hawa.
Wata majiya ta bangaren tsaro ta shaida wa shafin Zagazola Makama cewa an cafke wanda ake zargin ne a wani wurin bincike da jami’an tsaro suka kafa a garin Yankara.
Majiyar ta ce Mannir Adam, wanda mazaunin ƙauyen Yankuzo ne da ke ƙaramar hukumar Tsafe, yana tukin babur mai launin ja nau’in Boxer a lokacin da jami’an tsaro suka tare shi domin bincike.
A cewar majiyar, binciken da aka yi wa babur ɗin ya kai ga gano harsasai 800 na bindigar AK-47 da aka ɓoye a cikin tankin man babur ɗin.
Majiyoyin tsaro sun bayyana kama matashin a matsayin wata muhimmiyar nasara a ƙoƙarin da hukumomi ke yi na dakile safarar makamai da harsasai zuwa hannun ƙungiyoyin masu aikata laifi da ke addabar al’ummomi a Zamfara da wasu jihohin da ke makwabtaka da ita.
Rahotanni sun kuma nuna cewa jami’an tsaro na ci gaba da bincike domin gano ko akwai wasu mutane ko ƙungiyoyi da ke da hannu a safarar harsasan.
