News
Mace Da Likitoci Suka Ayyana Ta Mutu Ta Farfaɗo A Hanya Yayin Da Ake Kai Ta Gida Domin Jana’iza
Wani lamari mai ban mamaki ya jawo hankulan jama’a bayan da wata mata da likitoci suka ayyana cewa kwakwalwarta ta daina aiki ta sake farfaɗowa yayin da ake kai ta gida domin shirya mata jana’izarta.
Rahotanni sun ce matar mai suna Vinita Shukla, wacce ke aiki a matsayin mai rubuce-rubuce a kotun gundumar Pilibhit da ke jihar Uttar Pradesh dake a ƙasar Indiya, ta kamu da matsananciyar rashin lafiya a gidanta.
Hobbasar Gwamna Abba Kan Tituna Da Sabbin Gadojin Birnin Kano
Mijinta Kuldeep Shukla ne ya garzaya da ita wani asibitin gwamnati domin samun kulawar gaggawa. Bayan likitoci sun duba halin da take ciki, sun tura ta zuwa wani asibiti a birnin Bareilly domin samu ƙarin kulawa.
A cewar mijin nata, daga baya ya kai ta wani asibiti mai zaman kansa inda aka saka mata na’urar taimaka wa mutum yayi numfashi (ventilator). Sai dai likitocin sun sanar da iyalanta cewa babu sauran fata na ceton rayuwarta, suna mai cewa kwakwalwarta ta daina aiki, tare da ba su shawarar su mayar da ita gida.
Bayan iyalanta sun sanar da ‘yan uwa a Pilibhit, aka fara shirye-shiryen jana’izarta yayin da ake jigilar ta cikin motar asibiti zuwa gida.
Sai dai yayin da motar ke kan hanya kusa da garin Hafizganj a Bareilly, ta bugi wani rami a hanya, abin da ya haifar da girgiza a cikin motar. Mutanen da ke cikin motar sun ce daga nan ne suka lura cewa Vinita ta fara nuna alamun ta na
Nan take aka kai ta wani asibiti mai zaman kansa a Pilibhit domin sake duba lafiyarta. Da farko likitocin asibitin sun yi jinkirin karɓar ta, amma daga baya suka amince su fara mata jinya .
Wani likitan kwakwalwa, Dr. Rakesh Singh, ya bayyana cewa akwai yiwuwar matsalar ta samo asali ne daga cizon maciji. A sakamakon haka, likitocin suka yi mata allurar maganin dafin maciji tare da wasu magunguna.
A cewarsa, cikin kusan sa’o’i 24 bayan fara jinya, halin da take ciki ya fara inganta. Daga bisani kuma aka tura ta zuwa birnin Lucknow domin ƙarin bincike daga ƙwararrun likitoci.
Rahotanni sun ce bayan kusan kwanaki 13 tana jinya, Vinita ta murmure gaba ɗaya kuma ta koma gidanta, inda yanzu take rayuwa cikin koshin lafiya..
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News4 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
