News
Harin Dakarun Soji Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar ‘Yan Ta’adda 74 A Borno
Dakarun Sojin Najeriya sun gano gawarwakin ‘yan ta’adda akalla 74 bayan wasu hare-hare da ta kai a yankin Arewa maso Gabas, a wani bangare na kokarinta na murkushe ‘yan tada kayar baya a Jihar Borno.
Hedikwatar Tsaro ta bayyana cewa dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun hallaka ‘yan ta’adda da dama tare da dakile wani hari mai sarkakiya da aka yi amfani da jirage marasa matuƙa (drones) wajen kai hari.
Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Ranakun Komawa Makaranta
Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Juma’a yayin gabatar da bayanan ayyukan soja na mako guda, daga 13 zuwa 19 ga watan Maris.
A cewarsa, bayan farmakin, dakarun sun gano gawarwakin ‘yan ta’adda 74 tare da kwato tarin makamai daga hannunsu.
Makamai da aka kwato sun haɗa da: Bindigogi ƙirar AK-47 guda 38, Bindigogi masu aman wuta na PKT guda 3 da kuma Bututun harba roka
Rahotanni na nuni dacewa sojojin sun kuma dakile wani yunkurin hari a Mallam Fatori da ke Ƙaramar Hukumar Abadam a Jihar Borno, inda aka kashe mayaka da dama, ciki har da wasu manyan kwamandojinsu.
Onoja ya ce dakarun sun kuma dakile yunkurin kai hare-hare a wasu sassa na jihohin yankin, musamman a ƙananan hukumomin Bama, Gujba da Kaga.
Ya kara da cewa jami’an tsaro sun kama wasu da ake zargi da samar wa ‘yan ta’adda kayan aiki da kuma bayar da bayanan sirri.
A cewarsa, haɗin gwiwar hare-haren sama da na ƙasa sun taimaka wajen dakile ayyukan ‘yan ta’adda a yankuna kamar Baga, Damboa, Buratai da Njimtilo.
Ya ce hakan ya rage ƙarfin mayakan ISWAP tare da tauye ikon su na sake kai hare-hare.
Rundunar sojin ta jaddada kudirinta na ci gaba da matsa lamba kan ‘yan ta’adda ta hanyar kai hare-hare da kuma karfafa tattara bayanan sirri, domin dawo da cikakken tsaro a yankin Arewa maso Gabas..
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
