News
Shugaban Kamaru Ya Naɗa Ɗansa A Matsayin Mataimakin Sa Kuma Shugaban Sojin Ƙasar
Shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya, ya naɗa ɗansa, Franck Emmanuel Biya, a matsayin Mataimakin Shugaban ƙasa tare da kuma Shugaban Rundunar Sojin ƙasar, matakin da ke haifar da muhawara mai zafi a fagen siyasar ƙasar.
Sanarwar, wadda aka fitar a ranar 4 ga Afrilu 2026, ta kuma bayyana cewa Franck Biya zai zama Wakilin Minista a Ma’aikatar Tsaro, abin da ke nuna ƙarin tasirinsa a harkokin tsaro da mulkin ƙasar.
An Kama Malamai 7 Kan Satar Amsa A Yayin Zana Jarrabawar Kwarewar Aiki A Jigawa
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Cameroon ke fuskantar rikicin siyasa, musamman bayan zaɓen shugaban ƙasa da ya janyo ce-ce-ku-ce da kuma zanga-zanga a wasu sassan ƙasar.
Hukumomi sun bayyana cewa shugaba Biya, mai shekaru 92, ya lashe zaɓen da kashi 54 cikin 100 na kuri’u. Sai dai babban ɗan takarar adawa, Issa Tchiroma Bakary, ya ƙi amincewa da sakamakon, yana mai zargin cewa an tafka magudi—a zargin da gwamnati ta musanta.
Paul Biya ya shafe shekaru da dama yana mulki tun bayan da ya gaji marigayi Ahmadou Ahidjo a shekarar 1982. Sai dai a yanzu yana fuskantar ƙarin suka daga ‘yan adawa da masu sa ido kan harkokin siyasa, waɗanda ke zarginsa da ƙara ƙarfafa ikon mulki ta hanyar haɗa iko na siyasa da na soja.
