Connect with us

News

Jami’an EFCC Sun Cafke Mutane 31 Da Ake Zargi Da Damfara Ta Intanet A Abuja ‎

Published

on

FB IMG 1775803444458

Jami’an Hukumar EFCC sun cafke mutane 31 da ake zargi da damfara ta intanet a wani sumame da ta kai a wata cibiyar horas da masu aikata laifukan yanar gizo (“Yahoo Academy”) da ke Becki Estate, Karu a Babban Birnin Tarayya Abuja.

An kama waɗanda ake zargin, ciki har da shugabanninsu biyu da ɗalibai masu koyon aikin ne yayin da suke karɓar horo kan yadda ake gudanar da damfara ta intanet. Kayayyakin da aka kwato sun haɗa da wayoyi, da kwamfutoci guda 18 da sauran na’urori.

Advertisement

Yan bindiga sun bukaci shanu 700 da tumaki 1,000 A Katsina

‎Binciken EFCC ya nuna cewa wasu daga cikin ɗaliban an jawo su ne daga Jihar Benue da alƙawarin samun aiki, amma da zarar sun isa cibiyar, sai aka ba su na’urorin sadarwa da kwamfutoci tare da fara horas da su yadda ake aikata damfara.

Advertisement

‎An kuma gano cewa masu tafiyar da cibiyar suna tsare ɗaliban a wurin, suna taƙaita motsinsu, tare da karɓe wayoyinsu domin hana su hulɗa da waje, yayin da ake yi musu hukunci na duka idan suka nuna rashin biyayya.

‎Hukumar ta ce za ta gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar ta kammala bincike kan lamarin.

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending