Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Fitar Da Sunan Mutum 48 Da Ake Zargi Da Ɗaukar Nauyin Ta’addanci

Published

on

Gwamnatin Tarayya, ta fitar da sunan mutane da ƙungiyoyi 48 waɗanda ake zargi da tallafa wa ayyukan ta’addanci a faɗin Najeriya.

Hukumar da ke sanya takunkumi ta Najeriya (Nigeria Sanctions Committee) ce, ta bayyana jerin sunayen a ranar Asabar, 11 ga watan Afrilu, 2026.

Advertisement

An Fara Tattaunawa Tsakanin Amurka da Iran A Pakistan

Sunayen ya ƙunshi ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyin da bincike ya nuna suna da alaƙa da ayyukan tada ƙayar baya.

Advertisement

Daga cikin waɗanda aka ga sunansu har da mambobin ƙungiyoyi irin su IPOB, Ansaru, da kuma ƙungiyar ISWAP.

Wasu daga cikin fitattun mutane da sunansu ya bayyana cikin jerin, sun haɗa da Simon Ekpa da Tukur Mamu.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa wannan matakin na ɗaya daga cikin ƙoƙarinta na gano tare da toshe hanyoyin da ake bi wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a Najeriya.

Hakazalika, Gwamnatin ta bayar da umarnin rufe asusun bankunan waɗanda cikin jerin sunayen da aka fitar..

Advertisement

 

Ga sunayensu cikin hotuna a ƙasa:

Advertisement

Screenshot 2026 04 11 at 4.54.43 PM 1376x696 1

Screenshot 2026 04 11 at 4.54.29 PM 1376x693 1

Screenshot 2026 04 11 at 4.54.08 PM 1376x692 1

Screenshot 2026 04 11 at 4.53.51 PM 1376x674 1

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending