Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Kama Mutane 21 Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

Published

on

655997128 4343576645923177 2430566680323764567 n 750x536

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) a Jihar Kano ta sanar da kama mutane 21 tare da kwace nau’ikan miyagun ƙwayoyi da makamai na gida, sakamakon samamen da ta gudanar a wasu yankunan jihar.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari, ya fitar, ya ce an gudanar da samamen ne a ranar 11 ga watan Afrilu, 2026, a wurare da dama da ake zargi da zama cibiyoyin safarar miyagun ƙwayoyi.

Advertisement

Fiye Da Mutane 1,100 Aka Sace A Arewacin Najeriya Cikin Watanni 4 – Amnesty

Wuraren da aka kai samamen sun haɗa da Filin Idi, Hotoro, Mariri, Fagge da kuma yankin Farm Center da ke kan titin Zariya.

Advertisement

Hukumar ta ce a yayin aikin, jami’anta sun samu nasarar cafke mutum 21 tare da ƙwato abubuwa daban-daban, ciki har da tabar wiwi, ƙwayoyin pregabalin, magungunan tari masu ɗauke da sinadarin codeine da kuma sinadarin roba da ake shaƙa domin maye. Haka kuma, an kwace wasu makamai na gida daga hannun waɗanda ake zargi.

Sanarwar ta ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda aka kama sun yi yunƙurin tserewa ko kai hari ga jami’an tsaro, amma jami’an sun yi amfani da dabaru wajen shawo kan lamarin tare da cafke su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending