News
Fiye Da Mutane 1,100 Aka Sace A Arewacin Najeriya Cikin Watanni 4 – Amnesty
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa akalla mutane 1,100 aka sace a Arewacin Najeriya tsakanin watan Janairu zuwa Afrilu 2026, tana mai gargadin cewa lamarin na nuna ƙara tsananta matsalar tsaro da gazawar hukumomi wajen kare al’umma masu rauni.
A cikin wata sanarwa, ƙungiyar ta ce waɗanda ake sacewa na fuskantar matsanancin tashin hankali. “Yawanci ana azabtar da su, ana barinsu cikin yunwa, ana yankewa sassa jikinsu, ana yi musu fyade, har ma ana tilasta musu kallon ko aikata ta’asa,” in ji ƙungiyar, tana mai cewa da dama daga cikin waɗanda aka sace na shafe watanni a tsare cikin mawuyacin hali.
Jami’an NDLEA Sun Kama Tsoho Dan Shekaru 93 Da likita Bisa Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
Daraktan Amnesty a Najeriya, Isa Sanusi, ya ce abin da ke faruwa a yanzu a Arewacin ƙasar ya zama babbar barazana ga rayukan jama’a, inda sace-sacen domin neman kuɗin fansa ya zama ruwan dare musamman a ƙauyuka da sansanonin ‘yan gudun hijira.
Ƙungiyar ta kuma nuna cewa hare-haren ba su tsaya kan sace mutane kaɗai ba, inda maharan ke kashe jama’a, wawashe dukiya da ƙone gidaje. Ta ce iyalai da dama na sayar da kadarorinsu ko tara kuɗi daga al’umma domin biyan fansa, yayin da waɗanda suka kasa biyan kuɗin ke fuskantar kisa ko ci gaba da azabtarwa.
Amnesty ta nuna damuwa kan illar da hakan ke yi wa ilimi, inda tsoron sace yara ya sa iyaye da dama ke cire ‘ya’yansu daga makaranta, musamman ‘yan mata, ko ma su tilasta musu yin aure da wuri domin rage haɗarin kamuwa da hare-hare.
Ƙungiyar ta zargi hukumomin Najeriya da gazawa wajen cika nauyin da kundin tsarin mulki da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa suka ɗora musu na kare rayuka, tana mai cewa wannan na nuni da karya haƙƙoƙin ɗan Adam.
Rahoton na zuwa ne bayan wasu hare-hare da suka auku a jihohi da dama. A Jihar Kebbi, an kashe akalla mutane 24 a ƙauyen Debe ranar 5 ga Afrilu, inda maharan suka kashe duk wanda suka gani tare da lalata gidaje, shaguna da coci.
A Jihar Benue kuwa, an kashe mutane akalla 17 a Mbalom yayin bikin Ista, inda sama da mutane 500,000 ke gudun hijira sakamakon hare-hare da ake yawan kaiwa.
Haka kuma a Katsina, ƙungiyar ta ce ‘yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare duk da ikirarin yarjejeniyar sulhu, yayin da a Jihar Filato, ta danganta kashe-kashen da ake yi da gazawar tsaro, tana mai cewa jami’an tsaro kan isa wurin ne bayan maharan sun riga sun tsere.
A ƙarshe, Amnesty ta ce rashin bincike da hukunta masu laifi na ƙarfafa rashin hukunci, tare da ba ƙungiyoyin ‘yan ta’adda damar ci gaba da aikata laifuka ba tare da tsoro ba.
Ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen wannan rikici, tabbatar da adalci, da kuma kare al’ummomin da abin ya shafa.
