News
Jami’an NDLEA Sun Kama Tsoho Dan Shekaru 93 Da likita Bisa Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta sanar da kama wani tsoho mai shekaru 93 tare da wani likita mai shekaru 69, bisa zarginsu da hannu a safarar miyagun ƙwayoyi, yayin da take ƙara zafafa samamen ta a faɗin ƙasar.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fitar, ya ce an kama tsohon mai suna Pa Friday Chigbu a gidansa da ke ƙauyen Umuagbaigba, a ƙaramar hukumar Osisioma ta jihar Abia, a ranar 7 ga Afrilu, 2026.
Amurka Da Iran Sun Gaza Cim Ma Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tattaunawarsu Ta Pakistan
Hukumar ta ce bayan gudanar da bincike a gidansa, jami’anta sun gano kilo 7.7 na tabar wiwi nau’in skunk. A cewar sanarwar, wanda ake zargin ya bayyana cewa ya daɗe yana amfani da tabar wiwi tun daga shekarar 1959, kafin daga bisani ya koma safararta a matsayin sana’a kimanin shekara guda da ta gabata.
A wani ɓangare na samamen, NDLEA ta kama wani ɗan ƙasar Ivory Coast mai suna Gohouri Michael, mai shekaru 41, a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano, dauke da kunshin koken guda 82 masu nauyin kilo 1.49.
Binciken da hukumar ta gudanar daga baya ya kai ga kama wani likita, Dr. C. Ofomata, mai shekaru 69, a jihar Ogun, wanda ake zargin yana da alaƙa da safarar ƙwayoyin tare da bayar da umarni ga wanda aka kama a filin jirgin sama. An kai shi Kano domin ci gaba da bincike.
Hukumar ta ce ta kuma kwato wasu ƙarin sinadarai daga hannun likitan da suka haɗa da gram 63 na promazepam da kuma allurai bakwai na promethazine.
