Connect with us

News

Wasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano

Published

on

FB IMG 1777298290224

Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari a kasuwar sayar da wayoyi ta Farm Center da ke jihar Kano a tsakar rana, lamarin da ya janyo tashin hankali da firgici a tsakanin ‘yan kasuwa da masu saye.

Shaidu daga wurin sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin kasuwar ne ba zato ba tsammani, inda suka rika dukan jama’a tare da amfani da makamai masu kaifi domin razana mutane.

Advertisement

Kungiyar Tuntuba Ta Dattawan K/H Garko Ta Bukaci Jam’iyun Siyasa Da Su Tsayar Da ‘Yan Takara Da Suka Chanchanta a Kowanne Mataki Da Zasu Wakilci Garko

An ce harin ya fi shafar wani bangare na kasuwar da ake kira Yoyo Plaza, inda ake hada-hadar sayar da wayoyi.

Advertisement

Wata majiya ta ce, maharan sun kuma rika kwace wayoyi da sauran kayayyaki daga hannun mutane, ciki har da masu wucewa a hanyoyin da ke kusa da kasuwar.

Rahotanni sun kuma nuna cewa ana zargin wasu daga cikin maharan sun fito ne daga wani taron siyasa da aka gudanar a yankin Kano ta Tsakiya, sai dai babu wata hujja ta hukuma da ta tabbatar da hakan zuwa yanzu.

Advertisement

Bayan faruwar lamarin, jami’an ‘yan sanda sun isa wurin domin shawo kan rikicin, inda suka tarwatsa maharan tare da dawo da zaman lafiya a yankin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu cikakken bayani kan asarar rayuka, amma an ruwaito cewa wasu mutane sun samu raunuka.

Advertisement

Hukumomi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending