Connect with us

News

Ƙungiyoyi 25 Sun Kalubalanci Shigar Ƙungiyar Da Suke Zargin Adawa Da Gwamnati Cikin Shirin GAVI A Kano

Published

on

Civil Society Organisation CSO (2)

Wasu ƙungiyoyi 25 masu rajin kare muradun al’umma a Jihar Kano sun aike da ƙorafi ga Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Labaran Yusuf, da Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko ta Jihar Kano, kan shigar da Maryam Garba Usman ta ƙungiyar Centre for Gender and Social Inclusion (CAGSI) cikin shirin rigakafin cutar shan-inna na GAVI da ake gudanarwa a jihar.

‎A cikin ƙorafin mai ɗauke da kwanan watan 12 ga Mayu, 2026, ƙungiyoyin sun bayyana CAGSI a matsayin ƙungiyar da ke yawan sukar manufofi da shirye-shiryen gwamnatin jihar Kano, lamarin da suka ce na iya haifar da tambayoyi kan sahihanci da rashin son kai a gudanar da shirin lafiya mai samun tallafin ƙasa da ƙasa.

Advertisement

Sojoji Sun Musanta Kashe Fararen-Hula A Harin Sama Da Aka Kai Kasuwa A Zamfara

‎An kuma aika da kwafin ƙorafin ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Farouk Umar Ibrahim, da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, tare da Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta jihar.

Advertisement

‎Masu ƙorafin sun ce dukkan shirye-shiryen lafiya masu tallafin ƙasa da ƙasa, musamman waɗanda suka shafi rigakafin cututtuka, suna buƙatar  gaskiya, ƙwarewa da kuma rashin nuna son kai daga dukkan waɗanda ke da hannu wajen aiwatar da su.

‎Sun jaddada cewa tarihin yaƙi da cutar shan-inna a Arewacin Najeriya ya nuna yadda amincewar jama’a ke taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar irin waɗannan shirye-shirye, yana mai cewa duk wani abu da zai jefa shakku kan sahihancin masu gudanar da shirin na iya rage haɗin kan al’umma.

Advertisement

‎Ƙungiyoyin sun buƙaci Ma’aikatar Lafiya da Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko ta jihar su gudanar da cikakken bincike kan yadda aka zaɓi mutanen da ke cikin shirin Solina GAVI Grant, tare da tabbatar da cewa an bi dukkan ƙa’idoji da tanade-tanaden da suka dace.

‎Haka kuma sun yi kira da a tabbatar cewa waɗanda ake bai wa damar gudanar da shirin suna da cikakken tsayuwar daka wajen cimma manufofin lafiyar jama’a ba tare da wata manufa ta daban ba.

Advertisement

‎Masu ƙorafin sun kuma yabawa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf bisa abin da suka bayyana a matsayin jajircewa wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kyakkyawan shugabanci wajen tafiyar da shirye-shiryen gwamnati da masu tallafin ƙasa da ƙasa.

‎Sun ce irin manyan ayyukan da gwamnatin ta aiwatar a ɓangaren lafiya, ilimi da bunƙasa rayuwar al’umma a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar na nuna muhimmancin kare mutuncin duk wani shiri da ke da alaƙa da rayuwar jama’a.

Advertisement

‎Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga Ma’aikatar Lafiya ko Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko ta jihar Kano dangane da ƙorafin.

‎Masu ƙorafin sun kuma yi zargin cewa ƙungiyar CAGSI ta taɓa shiga ayyukan da suka haɗa da suka ga manufofi da shirye-shiryen gwamnatin jihar Kano tare da wasu ƙungiyoyin da suke kallon masu adawa da gwamnati ne a jihar.

Advertisement

IMG 20260514 WA0001

IMG 20260514 WA0002

IMG 20260514 WA0003

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending