News
An Kama Wata Matashiya Mai Shekaru 27 Bisa Zargin Satar Jariri A Asibiti A Zamfara
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta kama wata matashiya mai shekara 27 bisa zargin satar wani jariri mai kwana 10 da haihuwa a Babban Asibitin Ƙaura Namoda.
Lamarin ya tayar da hankalin jama’a ne bayan ɓacewar jaririn daga asibitin, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka shiga aikin bincike cikin gaggawa domin gano inda aka kai shi.
Kano: Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari A Gwarzo
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya bayyana cewa bayan samun rahoton faruwar lamarin, hedikwatar ’yan sanda ta Ƙaura Namoda ta fara gudanar da bincike tare da gayyatar jami’an asibitin da suke bakin aiki a lokacin domin amsa tambayoyi.
Ya ce bayanan da jami’an asibitin da wasu mazauna yankin suka bayar sun taimaka wajen gano inda aka kai jaririn.
“A sakamakon haɗin kan jama’a da sahihan bayanan da aka samu, jami’anmu sun gano jaririn a wata ruga mai suna Kogin Audu da ke Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda tare da kama wadda ake zargi,” in ji DSP Yazid.
Ya ƙara da cewa an ceto jaririn cikin ƙoshin lafiya kuma an mika shi ga iyayensa bayan kammala binciken farko.
Rundunar ta bayyana sunan wadda ake zargin da Asmau Nasiru, inda ta ce tana tsare a hannun ’yan sanda domin ci gaba da bincike kan lamarin.
Kazalika, Kakakin rundunar ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, Ahmad Muhammad Bello, ya yaba wa al’ummar jihar bisa haɗin kan da suka bayar wajen samar da bayanan sirri da suka taimaka wajen ceto jaririn cikin gaggawa.
Ya jaddada kudirin rundunar na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da yaƙar duk wani nau’in laifi a faɗin jihar.
Aminiya
