Connect with us

News

Rushewar Gini Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 5 A Abuja

Published

on

Building collapse 768x518 (1)

Akalla mutum biyar sun rasa rayukansu yayin da aka ceto wasu mutum 10 da rai bayan wani gini mai hawa uku da ake ginawa ya rushe a yankin Durumi 3 kusa da Kasuwar Gudu a Abuja.

Lamarin ya faru ne da safiyar Asabar, inda jami’an agajin gaggawa suka garzaya wurin domin gudanar da aikin ceto, yayin da ake zargin har yanzu akwai wasu mutane da suka maƙale ƙarƙashin baraguzan ginin.

Advertisement

Rushewar Gini Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 5 A Abuja

Mai bai wa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike shawara kan harkokin yaɗa labarai da sada zumunta, Mista Lere Olayinka, ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Advertisement

Ya ce ginin da ya rushe yana kusa da yankin Gaduwa Estate a gundumar Gudu, inda jami’an ceto ke ci gaba da laluben waɗanda ake kyautata zaton suna ƙarƙashin baraguzan.

Sanarwar ta ce Ministan Abuja ya bayar da umarnin gaggauta bai wa duk waɗanda abin ya shafa kulawar lafiya kyauta.

Advertisement

Sakatariyar harkokin lafiya da muhalli ta gwamnatin Abuja, Dakta Adedolapo Fasawe, ta kai ziyara wurin da lamarin ya faru domin duba yadda ake gudanar da aikin ceto da kula da waɗanda suka jikkata.

Ta bayyana cewa jami’an lafiya da na ceto na aiki cikin mawuyacin hali wajen bincike da zakulo waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Advertisement

A lokacin haɗa wannan rahoto, jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, jami’an tsaro, ma’aikatan lafiya da masu aikin sa-kai na ci gaba da aikin ceto, yayin da mazauna yankin suka taru cikin alhini suna jiran samun karin bayani kan lamarin.

 

Advertisement

 

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending