Connect with us

News

GOMBE: ’Yansanda Sun Cafke Saurayi Kan Yunƙurin Hallaka Budurwarsa Da Guduma

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama wani mutum mai suna Musa Adamu, mai shekaru 35, bisa zargin kai wa budurwarsa hari da guduma tare da yunƙurin kashe ta a unguwar Pantami da ke cikin birnin Gombe.

Lamarin, wanda ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na dare, ya bar matar da munanan raunuka, sai dai ta tsira bayan ta yi ihun neman taimako wanda ya jawo hankalin maƙwabta suka kai mata ɗauki.

Advertisement

Ana Zargin ‘Yan Mata Na Sayar Da ‘Kwayayan Haihuwarsu’ Domin Sayan Manyan Wayoyi A Filato

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa wanda ake zargin, mazaunin unguwar Riyal, ya tsallaka katangar gidan matar kafin ya kutsa cikin ɗakinta ba tare da izini ba.

Advertisement

Ya ce bayan shiga gidan, wanda ake zargin ya bugi matar da gudumar ƙarfe tare da ƙoƙarin shaƙe ta da igiyar USB. Haka kuma, ana zarginsa da kwashe kuɗi kimanin Naira 100,000 daga gidan.

“Da matar ta fara ihu, maƙwabta sun yi gaggawar kai ɗauki, lamarin da ya sa wanda ake zargin ya tsere daga wurin kafin daga bisani jami’an ’yan sanda su cafke shi,” in ji kakakin rundunar.

Advertisement

DSP Buhari ya ce an garzaya da matar zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci, inda daga baya aka sallame ta bayan samun sauƙi.

Binciken farko da rundunar ke gudanarwa ya nuna cewa wanda ake zargin ya taɓa neman matar ta ba shi kuɗi, amma ta ƙi amincewa da buƙatarsa, abin da ake zargin na iya kasancewa ɗaya daga cikin abubuwan da suka haddasa harin.

Advertisement

Rundunar ta kuma ce ta ƙwato gudumar da ake zargin an yi amfani da ita wajen kai harin da kuma igiyar USB da ake zargin an yi ƙoƙarin amfani da ita wajen shaƙe matar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chosu, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma tare da ɗaukar matakan doka a kan masu aikata laifuka.

Advertisement

 

 

Advertisement

Aminiya

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending