News
Gwamnan Kano Ya Yi Sabbin Naɗe-Naɗe Da Sauye-Sauyen Mukamai A Gwamnatinsa
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da sabbin naɗe-naɗe da sauye-sauye a mukaman wasu masu ba shi shawara na musamman, a wani yunƙuri na ƙara inganta harkokin mulki da tabbatar da ingantaccen aiki a gwamnatinsa.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Gwamnan Kano Ya Yi Sabbin Naɗe-Naɗe Da Sauye-Sauyen Mukamai A Gwamnatinsa
Sanarwar ta ce an soke mukaman Mai Ba Gwamna Shawara kan Harkokin Cikin Gida da kuma Mai Ba Gwamna Shawara kan Ofishin Abuja, inda aka mayar da waɗanda ke riƙe da mukaman zuwa wasu sabbin nauyin aiki.
A ƙarƙashin sauye-sauyen, an naɗa Habiba Mustapha Barwa a matsayin Mai Ba Gwamna Shawara kan Ayyuka na Musamman da suka shafi Mata, yayin da Umar Uba Akawu ya zama Mai Ba Gwamna Shawara a Ofishin Majalisar Zartarwa kan Harkokin Siyasa.
Haka kuma, an sauya wa Akibu Isa Murtala aiki zuwa sashen kula da ma’aikata, Ibrahim Adam zuwa harkokin sadarwar zamani, yayin da Nasiru Isa Dikko ya koma bangaren tallafawa da bunƙasa rayuwar al’umma.
Gwamna Yusuf ya kuma amince da naɗin Bello Nuhu Bello a matsayin Mai Ba Gwamna Shawara kan Mulki, Ahmed Muhammad Aruwa a matsayin Mai Ba Gwamna Shawara kan Yaɗa Labarai, Buhari Sule Kura a matsayin Mai Ba Gwamna Shawara kan Ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu, da Yahuza Ado Yankaba a matsayin Mai Ba Gwamna Shawara kan Harkokin Tashoshin Mota.
Sauran sabbin waɗanda aka naɗa sun haɗa da Ahmed Tijjani Musa, Ibrahim Hamisu Rimi, Mustapha Abdullahi Rabiu Kura, Injiniya Bashir Abdullahi Kutama, Naziru Abdullahi Karaye da Tahir Ado Rabi’u.
Gwamnan ya buƙaci sabbin waɗanda aka naɗa da su yi aiki cikin gaskiya, riƙon amana da jajircewa domin tabbatar da ci gaban jihar da kyautata rayuwar al’ummar Kano.
