News
Mamakon Ruwan Sama Da Iska Mai Ƙarfi Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Kaka Da Jikarta A Bauchi
Mutum biyu, kaka da jikarta, sun rasa rayukansu sakamakon mamakon ruwan sama da ya zo tare da iska mai ƙarfi a ƙauyen Bara da ke Ƙaramar Hukumar Kirfi a Jihar Bauchi.
Waɗanda suka rasu sun haɗa da Aisha Sagir mai shekaru 50 da kuma jikarta, Aisha Shuaibu mai shekaru huɗu, waɗanda dukkansu mazauna Unguwar Katsinawa ne da ke ƙauyen Bara.
Lamarin ya kuma haddasa lalacewar gidaje da kadarori masu yawa, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin jimami da alhini.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta, SP Nafiu Abubakar, cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
A cewar sanarwar, bala’in ya afku ne a ranar Talata lokacin da aka yi ruwan sama mai ƙarfi tare da iska mai ƙarfi, wanda ya haddasa asarar rayuka tare da jawo mummunar barna ga gidaje da sauran dukiyoyin al’umma a yankin.
Rundunar ta bayyana alhininta kan rasuwar mutanen tare da jajanta wa iyalansu da al’ummar ƙauyen Bara bisa wannan babban rashi.
Mazauna yankin sun bayyana damuwa kan yawaitar aukuwar bala’o’in da ke da nasaba da ruwan sama a lokacin damina, inda suka yi kira ga hukumomi da su ƙara ɗaukar matakan kariya da wayar da kan jama’a domin rage asarar rayuka da dukiyoyi a nan gaba.
