News
ZAƁEN 2027:Wasu ‘Yan Takarar Gwamna Sun Kashe Naira Biliyan 30 A Zaɓen Fidda Gwani — EFCC
Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa wasu ’yan takarar gwamna a Najeriya sun kashe tsakanin Naira biliyan 20 zuwa 30 wajen neman nasara a zaɓukan fidda gwani na jam’iyyunsu gabanin babban zaɓen 2027.
Olukoyede ya yi wannan bayyana ne a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, yayin da yake gabatar da lacca a taron farko na jerin manyan baƙi da Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya da Dabarun Tsaro (CPSS) ta Jami’ar Ilorin ta shirya, mai taken: “Rage Barazana da Haɗa Masu Ruwa da Tsaki Domin Gudanar da Zaɓen 2027 Cikin Lumana da Sahihanci a Najeriya.”
Oshiomhole Ya Nemi a Kama Tsohon Shugaban NNPCL, Mele Kyari
Ya ce yawaitar kashe maƙudan kuɗaɗe a harkokin zaɓe na barazana ga tsarin dimokuraɗiyya tare da ƙara haifar da cin hanci da rashawa a hukumomin gwamnati.
A cewarsa, yawan kuɗaɗen da ake kashewa domin samun nasarar zaɓe kan sanya waɗanda suka ci zaɓe neman hanyoyin dawo da abin da suka kashe bayan sun hau kan mulki, lamarin da ke haddasa karkatar da dukiyar jama’a.
“Kasuwancin ƙuri’u yana raunana tushen shugabanci nagari saboda yana lalata tsarin zaɓen shugabanni. Waɗanda suka kashe kuɗaɗe domin samun mulki na iya fi mayar da hankali wajen dawo da abin da suka kashe maimakon yi wa jama’a aiki,” in ji shi.
Shugaban na EFCC ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da yaƙi da sayen ƙuri’u da sauran hanyoyin amfani da kuɗi wajen karkatar da sahihancin zaɓe.
Ya bayyana cewa hukumar ta kama mutane da dama a sassan ƙasar nan bisa zargin sayen ƙuri’u da aikata wasu laifukan zaɓe, inda aka samu nasarar gurfanar da wasu tare da yanke musu hukunci.
Olukoyede ya ce daga cikin waɗanda aka gurfanar akwai ’yan siyasa, jami’an zaɓe da kuma wasu ’yan ƙasa da aka samu da hannu a aikata laifukan da suka shafi zaɓe.
Ya kuma yi gargadin cewa rashin hukunta masu karya dokokin zaɓe na iya yin illa ga dimokuraɗiyya da zaman lafiyar ƙasa, yana mai jaddada cewa babu wanda ya kamata ya kasance sama da doka.
