Connect with us

News

IGP Disu Ya Haramta Wa Jami’an ’Ƴansanda Yin Harkoki A Soshiyal Midiya Ba Tare Da Izini Ba

Published

on

Olatunji Disu

Babban Sufetan ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya haramta wa jami’an rundunar gudanar da ayyuka a kafafen sada zumunta ba tare da samun sahalewar hukumomin da abin ya shafa ba.

Sabon umarnin ya shafi ƙirƙirar bidiyoyi, gudanar da shirye-shiryen kai tsaye (live), wallafa abubuwan nishaɗi ko na barkwanci, da kuma duk wani aiki na neman kuɗi ta kafafen TikTok, Instagram, Facebook, YouTube da sauran dandalan sada zumunta, muddin jami’in na amfani da matsayinsa a matsayin ɗan sanda.

Advertisement

Shugaba Tinubu Ya Aike Da Kudirin Dokar Kafa ‘Yansandan Jihohi Ga Majalisar Dattawa 

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa ta samu wata takarda mai kwanan watan 22 ga Yuni, 2026, wadda ta ƙunshi umarnin da kuma gargadin hukunci mai tsauri ga duk jami’in da aka samu da karya dokar.

Advertisement

Takardar ta bayyana cewa duk wanda ya saɓa wa umarnin zai iya fuskantar dakatar da aiki nan take, riƙe albashi, rage matsayi, kora daga aiki, ko kuma gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin aikata babban laifi.

A cikin takardar mai lamba SB:4065/IGP.SEC/FHQ/ABJ/VOL.1/11, an aike da umarnin daga ofishin Babban Sufetan ’Yan Sandan da ke Abuja zuwa ga shugabannin sassa, kwamandojin shiyyoyi, kwamishinonin ’yan sanda na jihohi da na Babban Birnin Tarayya, domin tabbatar da aiwatar da shi a dukkan sassan ƙasar.

Advertisement

Takardar ta ce Babban Sufetan ’Yan Sandan ya nuna damuwa kan yadda wasu jami’ai ke amfani da kafafen sada zumunta wajen ƙirƙirar bidiyoyi da wallafa wasu abubuwa da suka shafi rundunar ba tare da neman izini daga hukumomin da suka dace ba.

A cewar takardar, matakin ya zama wajibi domin kare mutunci da ƙwarewar rundunar, tare da tabbatar da cewa duk wani saƙo ko bayani da ya shafi aikin ’yan sanda yana tafiya ne daidai da ƙa’idoji da dokokin aikin rundunar.

Advertisement

Haka kuma, rundunar ta umarci dukkan kwamandoji da shugabannin sassa da su tabbatar da bin umarnin ba tare da sassauci ba, tana mai jaddada cewa duk wanda aka kama da karya dokar zai fuskanci hukuncin da ya dace ba tare da nuna son kai ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending