Uncategorized
An Sanya Ranar Ɗaurin Auren Lawan Garba da Maryam Sulaiman Sankara
Iyalan marigayi Alhaji Garba Mai Gishiri PZ da kuma iyalan Alhaji Sulaiman Isah Sankara sun gayyaci ‘yan uwa, abokai da daukacin al’umma domin halartar auren ‘ya’yansu, Lawan Garba (Namaka Fagge) da Maryam Sulaiman Sankara.
A cewar sanarwar gayyatar, za a gudanar da Fatiha ranar Asabar, 11 ga Yulin 2026, da misalin karfe 2:00 na rana, a Babban Masallacin Sankara da ke Jihar Jigawa.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa za a fara taruwa daga karfe 11:00 na safe a gida mai lamba 79, Titin Kabobo, Fagge ‘C’, kusa da Layin ‘Yan Katifa, Fagge, kafin a tafi wajen daurin auren
Iyalan ma’auratan sun bukaci duk wanda ba zai samu damar halarta ba da ya sanya ma’auratan cikin addu’o’insa, tare da yi musu fatan Allah Ya albarkaci aurensu, Ya ba su zaman lafiya, soyayya da zuri’a ta gari.
An kuma bayyana lambobin waya domin karin bayani ko tabbatar da halarta, kamar yadda ke cikin katin gayyatar bikin.
-
News2 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News3 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News3 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
