Connect with us

News

Wani Mutum Ya Hallaka Matarsa Har Lahira Saboda Ta Ƙi Dafa Abinci 

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta kama wani mutum mai suna Musbahu Amadu, mai shekara 30, bisa zargin dukan matarsa har ta mutu a unguwar Yahaya da ke Agyaragu, Ƙaramar Hukumar Obi ta jihar.

Kakakin rundunar, SP Ramhan Nansel, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Jami’an NDLEA Sun Cafke ‘Yar Afirka Ta Kudu Da Hodar Iblis Filin Jirgin Sama A  Abuja

Ya ce ana zargin Musbahu ya lakada wa matarsa mai shekara 20 duka ne bayan wata saɓani da ya shiga tsakaninsu, wanda ake zargin ya samo asali ne bayan matar ta ƙi dafa masa abinci.

A cewarsa, bayan samun rahoton lamarin a Ofishin ’Yan Sanda na Agyaragu, jami’ai suka garzaya wurin tare da kama wanda ake zargin.

Nansel ya ce yayin da ake yi masa tambayoyi, Musbahu ya amsa cewa ya aikata hakan ne cikin fushi, inda ya bayyana cewa gardamar da ta shiga tsakaninsu ta rikide zuwa faɗa, wanda daga bisani ya yi sanadin mutuwar matar.

Advertisement

Ya ce ma’auratan sun yi shekara shida da aure, kuma sun bar yara biyu, ɗa namiji da ɗiya mace.

Sanarwar ta ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, CP Shetima Jauro Mohammed, ya ba da umarnin a miƙa shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Lafia domin gudanar da cikakken bincike.

 

 

 

CHANNELSTV 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending