Connect with us

News

Kungiyar TMS Ta Shigar Da Korafi Kan Zargin Shugaban Karamar Hukumar Kabo Da Muzgunawa Tafiyar

Published

on

IMG 20260813 230843 181
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Kungiyar tafiyar Tinubu Maliya Shonikan Organisation (TMS) ta shigar da ƙorafi ga shugabancin jam’iyyar APC a Jihar Kano, inda ta yi zargin cewa ana cin zarafi tare da tsoratar da wasu daga cikin mambobinta da masu riƙe da mukaman siyasa a Ƙaramar Hukumar Kabo.

Ƙungiyar ta ce matakan da ake zargin an ɗauka sun biyo bayan halartar wasu daga cikin mambobinta da shugabannin siyasa wani taron da TMS ta shirya a Kano.

Kwamishinan Yaɗa Labaran Kano, Waiya Ya Samu Lambar Yabo Ta Ƙasa Kan Ƙwarewar Yaɗa Labarai A Lokutan Rikici ‎

A cikin ƙorafin da Shugaban TMS na Jihar Kano, Nura Abdullahi Bagwai, Esq., ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta zargi Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo, Hon. Lawan Najume Kabo, da sauke Sakataren Ƙaramar Hukumar, Abba Salisu Mewake Garo, tare da wasu masu riƙe da mukaman siyasa, bayan sun halarci ƙaddamarwa da bikin rantsar da shugabannin TMS da aka gudanar a Kano ranar 9 ga Agusta, 2026.

TMS ta bayyana taron a matsayin wani taron wayar da kan jama’a cikin lumana, wanda aka shirya domin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, jam’iyyar APC da kuma manufofin Renewed Hope Agenda.

Kungiyar ta buƙaci shugabancin APC a Kano da ya gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen, tare da tabbatar da ko matakan da ake zargin an ɗauka sun yi daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC da kuma ƙa’idojin dimokuraɗiyyar cikin gida.

Advertisement

Haka kuma, TMS ta nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin ƙoƙarin sanya wasu shugabannin siyasa su nesanta kansu daga ƙungiyar saboda halartar tarurrukanta.

Saboda haka, ƙungiyar ta yi kira ga Shugaban APC na Ƙasa da shugabancin jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Yamma da su gaggauta shiga tsakani domin warware lamarin, dakile duk wani nau’in cin zarafi ko tsoratarwa, tare da tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya tsakanin mambobin jam’iyyar.

TMS ta jaddada cewa tana ganin bambancin ra’ayi da halartar tarukan siyasa a matsayin wani ɓangare na harkokin dimokuraɗiyya, tana mai cewa bai kamata hakan ya zama dalilin cin zarafi ko hukunta wani ɗan jam’iyya ba.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu martanin Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo, Hon. Lawan Najume Kabo, ko shugabancin APC na Jihar Kano kan zarge-zargen da TMS ta gabatar ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending