Connect with us

News

NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero

Published

on

IMG 20260923 115010 491

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta ce za ta fara shirye-shiryen sake fafutukar neman sabon ƙarin mafi ƙarancin albashi gabanin shekarar 2027, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa.

Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero, ne ya bayyana hakan a wajen taron wakilan Ƙungiyar ma’aikatan hukumomin gwamnati da ƙwararru ta AUPCTRE karo na bakwai da aka gudanar Jihar Kano.

Akalla Mutane 259 Ne Suka Mutu Sakamakon Zazzabin Lassa A Najeriya

Ajaero ya ce cire tallafin man fetur da kuma faduwar darajar Naira sun haifar da ƙarin tsadar rayuwa, tare da rage ƙarfin sayen kayan masarufi da albashin ma’aikata.

Ya ce bitar mafi ƙarancin albashi na gaba bai kamata ta kasance kawai domin cika abin da doka ta tanada ba, sai dai ya kamata ta yi la’akari da halin tattalin arzikin ƙasa da kuma ainihin abin da ake kashewa wajen rayuwa.

A cewarsa, ma’aikata ba sa iya jure hauhawar farashin kayan sufuri, man fetur da sauran muhimman kayayyaki da albashin da darajarsa ta ragu sosai sakamakon hauhawar farashin kayayyak

Advertisement

NLC ta kuma yi kira ga gwamnati da ta biya wasu ma’aikata kuɗaɗen Peculiar Allowance da kuma Wage Award da ake bin su, tana mai cewa waɗannan hakkoki ne da aka cimma yarjejeniya a kansu, ba kyautar gwamnati ba ce.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending